Dr Femi Ɗan Asabe (uba bahaushe uwa bayarba) ya karɓi takardar "call up letter" zuwa NYSC da niyyar hutawa sosai wannan shekarar. An ci ƙaniyar sa sosai a wajen "internship" inda ya aikatu kamar bawan rumawa.
Saboda haka tun a "orientation camp" ya nemi a kai shi garin da ake hutawa domin ya murmure daga uƙubar da ya gani a wajen "attachment". An tura shi ƙaramar hukumar "Rafin Zinari" inda ke dab da iyaka da ƙasashe biyu dake maƙwabtaka da ƙasar nan.
Dr Ɗan Asabe bai daɗe da kama aikin ba yayi kiciɓis da Zinatu 'yar kwalejin ilimi wadda ake kiki-kakan yi mata aure a gidansu ita kuma ta nace sai ta gama karatu.
Zina baƙar mace ce sosai mai ƙaramin jiki abun da marubuci ke kira 'yar shila a hausance ko kuma "petite" a turance. Mace ce mai ɗan karen kyau ga hanci, manyan idanu leɓɓa manya manya da dogon wuya. Amma wannan ba shi kaɗai
ne yasa Zina fice ba, Zinatu akwai kwarkwasa, wato marmaɗi, iya zolaya, wasa da dariya da iya jan hankalin namiji.
Ɗan Asabe ya haɗu da Zina ne lokacin da ta shigo asibiti karɓar medical report wanda zata kai makaranta(F.C.E) shi kuma ya nuna mata so. Ya ga yarinya ta ɗau wanka tana masa magana tana marmaɗi da dawwamammen kallo kuma tana cin cin gam("kas kas kas"), ga shi ta shafa gazar kalar azurfa a kan manyan leɓɓanta baƙaƙe wanda yasa Dr Ɗan Asabe ya dugunzuma ya ruɗe!
Zinatu kuwa tace "ai faɗuwa
ta zo daidai da zama, tunda kana sona ai sai ka fito. Ɗan Asabe kuwa ya nuna mata a dai fara wayewa da juna, ayi soyayya tukun, ita kuma ta ce faufau ko ɗan
alif ɗinta ba zai taɓa ba sai in an ɗaaura musu aure.
Ɗan Asabe yayi ta yi mata hidima domin ya ciwo kanta amma abun ya ci tura. Abokan Zinatu sun ce ma Zina ta manta da Ɗan Asabe ta yi aurenta idan ba zai fito ba. Haka kuwa aka yi ma Zina aure ana masha'a har ana yima Ɗan Asabe zambo kala-kala wajen biki bada sanin cewa murna na kan komawa ciki ba.